Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilin komawar Zaki gidan sa

Published

on

A yayin da aka samu nasarar komawar  Zakin nan Kejin sa da kan sa da safiyar yau.

Al’amuran sun fara komawa dai-dai a cikin gidan adana namun dajin dake nan Kano.

Rahotanni sun tabbatar da cewar mai kula shi ne yayi masa kiranye tare da yi masa ‘yan dabaru.

 

Da karfe 6:55 na safiyar yau litinin ne Zakin da ya kwace a gidan adana namun daji a ranar

Asabar da ta gabata ya koma kejin sa, bayan da ya yi tirjiya wajen kin shiga

Kejin na sa lokacin da ake kokarin mayar da shi bayan dawowa daga Jihar Nasarawa.

 

Tun a daren jiya ne dai Zakin ya bazama daga Kejin Jimuna Zuwa na Awaki wadanda daga nan ne kuma ake zargin cewa ya cinye Jimuna guda 1.

 

A lokacin da ake kokarin yi masa allurar kashe jiki bayan

gayyato kwararru daga babban birnin tarayya Abuja, yayin da jami’an ‘yan sanda suka yi

wa wajen kawanya don tabbatar da cewa Zakin bai yi barna ba.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!