Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yunwa ce ta sa Zaki ya bijire

Published

on

Shi wannan zaki dai ana zaton yunwa ce ta sa yayi bore domin kuwa a lokacin da aka kai shi jihar Nassarawa domin yin bajin kolin albarkatun gona a makon da ya gabata wanda kafin tafiya dai zakin an tsagaita bashi abinci domin a samu damar sarrafa shi.

 

Da suka dowa gida Kano a ranar asabar din da ta gabata wato 18 ga wannan wata, sai zaki ya kufce a lokacin da ake kokarin saka shi a gidan sa,Ya kubuce tare da kutsawa cikin wani garken awaki da ke cikin gidan namun dajin inda ya hallaka awaki guda hudu.

 

Bayan  da yayi kalaci da guda daya inda guda biyu daga cikin akuyoyin tsoro ya hallakasu.

 

Manajan darakta na hukumar gidan Zoo , Alh Saidu Gwadabe Gwarzo ya alakanta bijirewar zaki a matsayi wani akasi da ba’a taba samun irinsa ba.

Zakin gidan Zoo ya kara bacewa

 

Har ila yau zakin dai ya hallaka jimina guda biyu wanda rahotanni suka bayyana cewar sun takale shi ne da fada, yayin da ya farmu su, inda guda da take kokarin kaucewa ta tsira da ranta bayan da ya kashe dayar.

 

Sai dai zuwa yanzu mahukunta basu kayyade kudin dabobbi da zakin ya hallaka ba.

 

Duk da haka ana ganin darajar zaki ta dararwa dabobbin da ya hallaka kasancewar zakuna biyu ne kadai a gidan Zoo kuma shine mafi kuruciya.

 

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewar zakin ya koma kejinsa ne ba tare da an tursasa shi ba da misalin karfe 6.50

 

Amma dai wata majiya a gidan namun dajin ta bayyana cewar kubucewar zakin na da alaka da yunwa sakamakon hana shi abinci a lokacin da aka tafi baje kolin kayan gona a jihar Nassarawan Najeriya gami da gajiya, wanda ta sa shi kansa zakin ya kasa sarrafa kansa.

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!