Labarai
Abunda ya kamata ku sani kan kasafin kudin badi
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sami rakiyar wasu daga cikin ‘yan Majlisar zartarwa na kasa wajen gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin badi, gahadakar majalisar dokoki ta kasa.
Shugaba Buhari wanda ya fara jawabi ga hadakar majalisun da misalign karfe 2 da minti 3 na ranar yau Talata, ya gabatarwa majalisun daftarin kasafin kudin badi da yah aura Naira Tiriliyan goma 10.
Tun da fari majalisar zartarwa ta kasa ta mika daftarin kasafin kudin badi bayan da ta tsara akan Naira Tirilyan 10 da miliyan bakwai yayin da su kuma ‘yan Majalisar suka kara zuwa Tiriliyan 10 da miliyan talatin da uku.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce daftarin gwamnatinsa ta tsara kasafin ne a kan kudin harajin kayayyaki da na VAT, a don haka ya zama tilas a kara yawan harajin daga kaso hudu zuwa 7.7
Hakan dai zai sanya gwamnati damar cike gibin fiye da naira tiriliyan biyu da ke kasafin kudin kasar da Muhammadu Buhari ya gabatatar a yau.
Muhammadu Buhari wanda ya gabatar da daftarin kasafin kudin a gaban zauren majalisar dokokin kasar, ya ce kasafin na 2020 ya haura na 2019 da kaso 9.7 cikin dari.
Yadda kasafin kudin kowace ma’aikata zai kasance
- Ma’aikatar Tsaro – naira biliyan 100
- Ma’aikatar ayyukan gona – naira biliyan 83
- Ma’aikatar Albarkatun ruwa – naira niliyan 82
- Ma’aikatar kula da Ilimi – naira biliyan 48
- Ma’aikatar Lafiya – naira biliyan 46
- Hukumar Raya Arewa maso gabas – naira biliyan 38
- Birnin tarayya – naira biliyan 28
- Hukumar kula da yakin Neja Delta – naira biliyan 24
- Sai kuma Majalisar dokoki – naira biliyan 125
- Ma’aikatar Shari’a – naira biliyan 110
- Ma’aikatar ayyuka da da gidaje – naira biliyan 262
- Ma’aikatar Sufuri – naira biliyan 123
- Hukumar ilmi a matakin farko UBEC – naira biliyan 112
Shugaba Buhari ya bukaci a baiwa ‘yan Najeriya mazauna Africa ta kudu kariya
Masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewar a bara dai a yayin gabatar da kasafin kudin bara an yi ta yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari Ihu kuma wannan shi ne karon farko da zauren majalisa na yayi ta Sowa sai Baba sai Baba.
Wannan dai alama ce dake nuna dagantakar zaman lafiya tsakanin majalisar zartarwa da ta ‘yan majalisar.
Rahotanni sun bayana cewar wannan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu ya gabatar da daftarin kasafin kudi a kan akari saboda alakar da ke tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.