Labarai
ACReSAL da FAO sun ƙaddamar da shirin farfaɗo da Kadada 350,000 na ƙasar noma da ta lalace
Gwamnatin tarayya da hukumar samar da wadataccen abinci na majalisar dinkin duniya FAO, da kuma shirin gwamnatin Kano na daƙile matsalar kamfar ruwa musamman a wuraren tsandauri watau ACReSAL.
Sun ƙaddamar da shirin farfaɗo da kimanin Kadada dubu ɗari uku da Hamsin na ƙasar noma da ta lalace a nan Kano.
Aikin tare da bayar da horo na musamman ga jami’an da za su riƙa sarrafa motocin burkiɗa ƙasa na zamani mai suna Delpino Plough da aka ƙaddamar a ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano zai kuma ƙunshi dasa bishiyu har ma da bai wa manoma aron filaye da riri da taki domin ƙara samar musu aikin yi.
Yayin ƙaddamar da aikin a yau Asabar, shugaban shirin ACReSAL na jihar Kano Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana cewa, wannan shiri na haɗaka, zai taimaka matuƙa musamman a fannin magance matsalolin ɗumamar yanayi da samar wa manoma ayyukan yi.
“Idan muka kammala wannan aiki, za mu nemi manoma da za mu ba su aron gonaki da kyautar iri da taki, idan suka yi noma na kamar shekara ɗaya ko biyu sai gonakin su dawo hannunmu ta haka ne za mu dasa bishiyu a wurin domin raya shi sosai,” inji shugaban shirin na ACReSAL na Kano.
Ya ci gaba da cewa, waɗannan manoma za mu ba su irin abubuwan da muke so su shuka musamman itatuwnmu na gida waɗanda za a iya yin amfani da su domin ci da na sha ko kuma sayarwa domin samun kuɗi.”
Malam Nasiru Yakubu, guda ne cikin mutane goma da suka karɓi horo kan sarrafa motar birkiɗa ƙasa, ya bayyana cewa, “Na zo ne daga hukumar kare muhalli ta jihar Bauchi, kuma Alhamdulillah na koyi abubuwa da dama a kan wannan mota, a haka za ka ganta kamar Tantan da muka saba amfani da ita, sai dai wannan ta na da bambanci matuƙa, domin ba ma taɓa ganin motar aiki irin ta ba.”
” Baturen da ya koya mana aiki da wannan mota ya yi ƙoƙari sosai, ya koya mana abubuwa da dama a kanta, ya koyar da mu yadda za mu kula da hali da yanayin da motar ke ciki tun kafin ma ka fara yin aiki da ita har zuwa lokacin kammalawa.”
Ya ci gaba da cewa,”Akwai littafi na musamman da aka tanada a cikin wannan mota duk lokacin da ka zo domin yin aiki da ita, dole ne za ka shigar da bayanan yadda ka same ta da aikin da ka yi da ita da kuma yadda ka ajiye ta bayan gama aiki, hakan zai taimaka musu wajen ganowa tare da gyara ta cikin sauƙi idan ta samu matsala,” inji Nasiru Yakubu.
Shi kuwa ƙwararrun mai bayar da horo daga shirin samar da ingantaccen abinci na majalisar dinkin duniya Mista Jamie Rixton, da ya yi bayani cikin harshen Turanci, ya bayyana cewa, ya ji daɗi bisa yadda ɗaliban nasa suka kasance masu hazaƙa da kuma nuna ƙwarewa a yayin ɗaukar horon.
Ya ce, “Ina da ƙwarin gwiwar cewa babu abinda ba za su iya yi da wannan mota ba, haka kuma muna so a duk lokacin da ta samu matsala kada a ce za a gyara ta, kawai a sanar da mu za mu zo ba tare da ɓata lokaci ba domin gyarawa saboda babu masu gyaranta sakamakon bambanci da ta ke da shi da sauran motocin noma.”
You must be logged in to post a comment Login