Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokoki ta yi zaman alhinin rashin mambanta

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta yi zama na musamman don nuna alhini da jimami bisa rasuwar guda daga cikin mambobinta Alhaji Halilu Ibrahim Kundila da ya rasu a ranar 7 ga wannan watan da muke ciki na Afrilu, sakamakon wata gajeruwar jinya.

Yayin zaman majalisar a yau Litinin bayan da ta dawo aiki daga hutun Sallah, shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana alhini bisa rasuwar ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazaɓar Bagwai da Shanono tare da yi masa addu’ar samun rahamar ubangiji shi da dukka waɗanda suka rasu.

Haka kuma ya Bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda kuma kyalekyalen duniya bai dame shi ba

Haka kuma shugaban majalisar, ya bayar da dama ga ɗaukacin wakilan zauren inda suka miƙa ta’aziyyarsu tare da bayyana irin zaman da suka yi da marigayin.

Daga bisani majalisar ta yi addu’o’in samun rahamar Mahalicci tare da yin addu’a ta musamman ga al’ummar da suka rasu a baya-bayan nan ciki har da Na’ibin babban masallacin Kano da marigayiya Hajiya Shekara da Saratu Gidado da aka fi sani da Daso da sauransu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!