Labarai
ACReSAL ya bude famfunan Burtsatse a yankunan Bichi da suka fi shekaru 40 babu ruwa
Gwamnatin jihar Kano karkashin shirinta na ACReSAL mai aikin daƙile matsalar kamfar ruwa da matsalolin sauyin yanayi musamman a wuraren tsandauri, ta samu nasarar bude wasu manyan rijiyoyin Burtsatse da ke bayar da kimanin Lita 22,500 masu amfani da hasken rana da ta samar ga al’ummar garuruwan Danya da Kyallin Bula a karamar hukumar Bichi da suka shafe fiye da shekaru arba’in suna fama da karancin ruwa.
Bude Famfunan na zuwa ne bayan kammala aikin samar da su a tsakanin ranakun Laraba da kuma Juma’ar nan bayan da gwamna Injiniya Abba Kabar Yusuf ya bayar da umarnin samar da rijiyoyin a ranar 24 ga watan jiya na Maris.
Da ya ke bude rijiyoyin, Shugaban shirin na ACReSAL da ya jagoranci aikin Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya ce, ”Ina farin cikin sanar da wanann gagarumin ci gaba a wadannan yankuna domin ganin mun magance matsalar karancin ruwa musamman a yankunan karkara karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ta hannun shirinmu na Kano ACRESAL.”
” Cikin gaggawa mai girma Gwamna ya umarce mu da kama wannan aikin gadan-gadan kuma mu tabbatar mun samar da ruwa da mafita mai dorewa ga wannan yanki musamman ga al’ummar Danya da Kyallin Bula, da sauran yankunan da ke fuskantar irin wadannan matsaloli.”
Haka kuma ya kara da cewa, ”Aikin samar da ruwan sha ga al’ummar garuruwan nan ya nuna wani gagarumin mataki a wannan fanni da kuma manufar gwamnatin jihar Kano na tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha ga kowa da kowa.”
Da ya ke yin jawabin godiya dangane da aikin Kansilan riko na yankin Malam Mudassir Lawan Liman Malikawa Garu, ya kuma roki gwamnatin jihar Kano da ta taimaka wajen sama musu asibiti ko da na sha ka tafi ne da makaranta da kuma masallaci har ma da karin wasu ababen more rayuwar.
Su ma wasu mazauna yankunan, sun bayyana farin cikinsu tare da yin fatan cewa, wannan aiki zai zamo a matsayin yankewar wahalhalun da suke sha na samun ruwan amfain yau da kullum da suka shafe shekaru da dama su na fama.
You must be logged in to post a comment Login