Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin Kwamishinoni da masu bashi shawara na musamman

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya rantsar da karin sabbin kwamishinoni guda hudu, da kuma manyan masu bashi shawara na musamman guda takwas da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano wanda Farfesa Sani Lawan Manumfashi zai jagoranta.

Hakazalika, gwamnan ya rantsar da mambobin hukumar kula da ayyukan majalisa dokokin jihar Kano wanda Hon. Gambo Sallau ya kasance shugaban hukumar.

Da yake jawabi yayin rantsar da su Gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabbin waɗanda aka naɗa da su kasance masu riƙon gaskiya da amana da kuma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Cikin sabbin kwamishinonin da aka rantsar, sun haɗa da Adamu Aliyu Kibiya ma’aikatar kasuwanci, sai Abduljabbar Umar Garko, ma’aikatar ƙasa da safayo, da kuma Shehu Aliyu Ƴarmedi ma’aikatar ayyuka ta musamman, Mustapha Rabi’u Kwankwaso ma’aikatar matasa da wasanni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!