Labarai
ActionAid: Gwamnatin Kano ta yaba da Irin ƙoƙarin ƙungiyoyi masu zaman kan su
Gwamna jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yaba da irin kokarin kungiyoyi masu zaman kansu Action Aid Nigeria da Dispute Resolution and Initiative Group (DAG) na tallafawa matasa da Mata sama da 300 a jihar Kano.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Alhaji Shehu Wada Sagagi ya bayyana hakan ne yayin bikin ba da tallafi da ƙungiyoyin ta bayar wanda ya gudana a ɗakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin Kano a ranar Litinin 04 Nuwamba 2023
Sagagi ya ce gwamnatin Injiniya Abba Kabir na yin kokari wajen taimakawa matasa da Mata a Kano domin dogaro da kai ta fannin sana’o’i da sassa daban-daban da za su iya sa su zama masu cin gashin kansu.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da hada kai da kungiyoyin wajen tallafa wa al’ummar jihar musamman a wannan lokaci na matsin rayuwa.
“Muna kira ga dukkan wa’inda suka ci gajiyar shirin da su tabbatar sun yi amfani da kayan aikin ta hanyoyi masu kyau wanda zai ba da sakamakon samun nasara wanda zai iya taimakawa matasa.
” A nata jawabin mataimakiyar daraktar kungiyar ActionAid ta Najeriya Hajiya Suwaiba Muhammad Dankabo ta ce kungiyar tana aiki ne tare da hadin kan mutanen da ke fama da talauci da wariyar launin fata don samun adalcin zamantakewa, daidaiton jinsi da fatara, sadaukar da kai wajen samar da adalci da dorewar rayuwa ga kowane mutum.
A nasa jawabin daraktan kungiyar Democratic Action Group na jihar Kano (DRDI-DAG) Dakta Mustapha Muhammad Yahaya ya ce mahalarta taron da suka fito daga kananan hukumomi shida jihar inda aka zabo su tare da horar da su kafin su ba su kayan aiki.
Dr Mustapha ya ci gaba da cewa shirin bayar da tallafi mai tsoka da gwamnatin jihar Kano zata mikawa mata da matasa 300 kayayyakin sana’o’in hannu da kudinsu ya kai miliyan arba’in.
Ya ci gaba da cewa, Matasa da Maza masu neman damar saka hannun jari a yawancin lokuta talauci, rashin aikin yi, warewar jama’a da rashin aikin yi suna samun rashin cancantar karatu da iyawa da basirar shawo kan wadannan matsaloli.
“An horar da wadannan mahalarta taron sarrafa Shinkafa, Tailo, sarrafa Man Groundnut inda aka zabo su daga kananan hukumomin Gwarzo, Gwale, Bebeji, Nasarawa, Tudun Wada da Bichi.
Idan za a iya tunawa shirin SARVE III shine ActionAid Nigeria da kuma kokarin DAG wanda Global Community Engagement and Resilience Fund ke tallafawa wanda aka sani da (GCERF).
You must be logged in to post a comment Login