Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Mun tallafawa manoma 366 da kayan aikin noma kyauta – SAA

Published

on

Manoma da dama a nan jihar Kano na ci gaba da kokawa kan matsalar da suke fuskanta na rashin gurin aje kayan amfanin gonar su da suke fuskanta.

Haka zalika manoman sun ce, sakamakon rashin gurin aje kayan amfanin gonar ta su yasa suka, samun lalacewar amfanin kayan gona.

kungiyar dake kawo cigaba akan harkokin noma sasakawa da kuma hadin gwiwar cibiyar bunkasa noma ta jihar Kano, KSADP karkashin tallafi bakin musulunci tace za ta tallafawa manoma maza da mata wajen inganta harkokin noman su da sarrafa amfanin su.
Shugaban shirin a nan Kano Alhaji Abdulrashid Hamisu kofar mata ne ya bayyana hakan yayin ziyara da kungiyar ta kaiwa manoman domin ganin irin ayyukan da sukayi a cikin shekara nan da muke shirin bankwana da ita ta 2023.
Kofar mata yace sun gudanar da wannan aiki ne domin kawo karshen rashin aikin yi a jihar Kano.

“mun gudanar da ayyuka iri iri da yawan su ya kai 3066 a kanan hukumomi 44 da suke jihar Kano inda mukai ziyara kanan hukumomi 15 da ku kamar yadda kuka gani”

Suma wanda suka amfana da tallafin maza da mata da suka koyi sana’o’i daban daban da ya hada kowa musu zazzaɓi shinkafa sarrafa kayan amfani gona kamar su tumatur da kuma kayan abinci da sauransu tare da basu inji kyauta sun yi karin haske kamar haka.
Kamar yadda daya daga cikin su Malama ta bayyana a karamar hukumar Bichi Rakiya Abdullahi.
“mun koyi yadda ake sarrafa waken soya zuwa garin domin gujewa lalacewae sa”.

A nasa bangaren shugaban hukumar NADA a nan jihar Kano ya bawa kungiyar ta Sasakawa ya yi kan irin ayyukan alheran da suke.
“Zamu saka ido akan duk wani da kungiyar sasakawa ta tallafawa zakuma mu hukuntar da duk wanda baiyi amfani da kayan ta hanyar da ta dace”

Kungiyar ta kai ziyara ƙanan hukumomi guda 15 cikin 44 da muke dasu a jihar Kano in da aka bude cibiyoyin dogaro da kai guda 17.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!