Labarai
Adamawa: Ƴan sanda sun cafke mutumin da ake zargi da yin garkuwa da mutane

Rundunar yan sandan Jihar Adamawa, ta cafke wani mutum da ake zargi da yin garkuwa da mutane, da ke cikin jerin sunayen mutanen da ake nema ruwa a jallo a jihar.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da jam’in yaɗa labarai na rundunar ƴan Sandan Jihar ta Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar a jiya Lahadi.
Sanarwar ta tabbatar da cewar an kama wanda ake zargin ne a Kasuwar Girei bayan samun bayanan sirri, inda jami’an ’yan sanda suka kai samame suka kama shi.
A cewar sanarwar, daga cikin abubuwan da aka samu a hannunsa akwai kuɗi naira 100,000, gasassun kaji da sauran kayan abinci da darajarsu ta kai kimanin naira 230,000.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa, Dankombo Morris , ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka gudanar da aikin, tare da jaddada kudurin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login