Labarai
ADC ta soki Tinubu bisa yin afuwa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi

Jam’iyyar adawa ADC ta soki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa yafe wa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a cikin jerin mutane 175 da suka amfana da afuwar shugaban ƙasa a shekarar da muke ciki ta 2025.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce wannan mataki yana lalata yaki da safarar miyagun ƙwayoyi, kuma yana bata suna da matsayin Najeriya a idon duniya.
Sai dai fadar shugaban kasa ta ce wannan afuwa ta bi matakan doka ne, kuma an yi la’akari da nadama da gyaran hali na wadanda abin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login