Connect with us

Labarai

ADC ta zargi INEC da kitsa hanyoyin hana ta tsayar da yan takara a zaɓen 2027

Published

on

Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar zaɓe  INEC, da shirya hanyoyin da za su hana ta tsayar da ‘yan takara a zaɓen 2027.

 

A cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar,Malam  Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce matakan da INEC ke ɗauka na iya hana ta shiga zaɓe gaba ɗaya, duk da cewa hukumar na cewa matakin na bin doka ne sakamakon shari’ar da ke gaban kotu.

 

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga matakin da INEC ta ɗauka na ƙin hulɗa  da ADC har sai an kammala shari’ar shugabancin jam’iyyar a kotun tarayya. 

 

Sai dai Jam’iyyar  ta ce wannan mataki na barazana ga ikon ta na cika sharuddan doka, musamman wa’adin kwanaki 21 da dokar zaɓe ta tanada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!