Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

AFCON 2022: A daina zargi shugaba Muhammadu Buhari kan ficewar Najeriya – Akwuegbu

Published

on

Tsohon dan wasan gaban Najeriya Ben Akwuegbu ya ce bai kamata a ci gaba da sukar shugaba Muhammadu Buhari kan rashin nasara da Super Eagles ta yi a hannun Tunisia da ci 1-0 a zagayen kasashe 16 na gasar cin kofin Afrika AFCON da ake bugawa a kasar Kamaru.

Zakarun gasar har sau uku Super Eagles sun dai samu nasarar wasanni uku na matakin rukunin da suke na D, da suka hada da nasara a da ci 1-0 a kan Egypt, da 3-1 a hannun Sudan sai kuma nasara da ci 2-0 a kan kasar Guinea-Bissau.

Tinda fari dai dan wasan Tunisia Youssef Msakni ne ya zura kwallo daya a ragar mai tsaran gida Maduka Okoye na Super Eagles a minti na 47 da wasan.

Kafin fafata wasanne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan wasa ta hanyar allon gani gaka wato ‘Zoom’ da nufin kara musu karfin gwiwa, amma kuma nasarar ta gaza samuwa da kungiyar.

Wanda hakan ya sa mutane da dama a Najeriya suke sukar shugaban bayan ganawar da ya yi da ‘yan wasan.

“Ficewar Super Eagles a gasar a iya cewa rashin daukar fafatawar da karfi ne, sakamakon dogara da sukai na matsalar ‘yan wasan Tunisia da suka kamu da cutar Covid-19,”

“Domin kuwa Super Eagles sun fara gasar da karfi da kuma gwanin ban sha’awa amma daga bisani suka samu tasgaro a gasar, wanda bai kamata zargin shugaba Buhari da wasu ‘yan Najeriya ke ci gaba da yi ba,” a cewar
Akwuegbu yayin ganawarsa da Completesports.

Tsohon dan wasan Stum Gratz da ke kasar Austria ya kuma nuna gamsuwar da yadda Eguavoen ya jagoranci kungiyar a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!