Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Tennis: Rafael Nadal ya lashe gasar Australia Open

Published

on

Dan wasan kasar Spain Rafael Nadal ya doke Daniil Medvedev a gasar Australian Open a wasab karshe da suka fafata a ranar Lahadi 30 ga watan Janairun 2022.

Nasarar ta bashi damar kasancewa namiji na farko da ya lashe Grand Slam har guda 21.

Dan wasan Nadal ya yi nasara ne da ci 2-6 da 6-7 da (5-7) da 6-4 6-3 7-5 wasan da ya gudana a birnin Melbourne na kasar Australia.

Wannan dai na zuwa ne bayan da tunda fari a ranar Asabar 29 ga watan Janairun 2022 ‘Yar wasa Ashleigh Barty ta yi nasarar lashe gasar ta Australian Upen karo na farko a tarihi.

Lamba ta daya a duniya ta yi nasarar ne da ci 6-3, da 7-6 da (7/2) a kan ‘yar kasar America Danielle Collins.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!