Kasuwanci
AFDB Na shirin tallafa wa fiye da manoma miliyan 2 a Nijar

Bankin raya Ƙasashen Afirka AFDB, ya sanar da shirinsa na tallafa wa manoma sama da miliyan biyu a Jamhuriyar Nijar, don bunƙasa harkar noma a ƙasar.
Muƙaddashin mataimakin shugaban bankin na Martin Fregene ne ya sanar da hakan, a lokacin da ya ziyarci Fira ministan Nijar kuma ministan tattalin arzikin ƙasar Mahaman Ali Lamine Zeine, a birnin Niamey.
Fregene ya ce a ƙarƙashin tawagarsa da suka ziyarci Nijar, akwai kwararru a ɓangaren noma da tattalin arziƙi, waɗanda za su taimaka wajen tsara yadda za a samu nasarar shirin.
Ya ce suna fatan nan da shekarar 2027 za a ƙaddamar da shirin, wanda zai taimaka wajen cimma manufofin shugaban ƙasar Abdourahamane Tiani, na ciyar da ƙasar gaba.
You must be logged in to post a comment Login