Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ahlan Cup: Kano Pillars ta je wasan karshe

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Kano pillars ta kai matakin wasan karshe a Gasar cin kofin shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano, Alhaji Sharu Rabi’u Alhan.

Kungiyar ta Kano Pillars takai matakin ne bayan data doke kungiyar kwallon kafa ta Elkanemi dake garin Maidugurin jihar Borno da ci 5-4 a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Wasan wanda ya gudana a ranar 9 ga watan Nuwambar 2021 da misalign karfe daya da rabi a filin wasa na tsohuwar Jami’ar Bayero dake Kano.

Tun da fari dai an tashi daga wasa Kano Pillars nada ci 2- yayin da Elkanemi keda 2.

Jim kadan bayan kammala wasan shugaban kungiyar ta Kano Pillars Alhaji Surajo Yahaya Jambul ya bayyana cewa wasan ya kayatar matuka ganin cewa Pillars ta sami nasara a wasan duk da cewa wasu na ganin akwai gyare-gyare a kungiyar.

A yammacin yau Kano Pillars za ta buga wasan ta na karshe da kungiyar Doma FC a filin wasa na tsohuwar jami’ar Bayero.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!