Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ahmad Musa zai iya yiwa Najeriya wasanni 140-Vincent Enyeama

Published

on

Tsohon Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Vincent Enyeama, ya ce yana fatan Kaftin din kungiyar Ahmad Musa zaiwa kasar nan wasanni 140.

Ahmad Musa, yanzu haka ya buga wasanni 98 a kasar nan.

 

A baya dai an bayyana cewar dan wasan ya buga wasanni 100 a wasan neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da ya wakilci kasar nan a wasan da Najeriya ta doke kasar Liberia da Cape Verde, inda daga baya hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta ce wasanni 98 Ahmad Musa ya bugawa Najeriya ba 100 ba.

Enyeama, ya ce ba wasanni 100 bama, zai iya yiwa kasar nan wasanni sama da 130 duba da lafiyar da yake da ita.

Ya kuma ce Ahmad Musa mutun ne da ya iya mu’amula da mutane musamman yadda yake jankowa a jikinsa tare da hadakan ‘yan wasan kungiyar ta Super Eagles, a cewar sa “Hakan ne yake Kara bawa kasar nan nasarori a wasannin da take”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!