Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jinƙai: Babban jojin Kano ya sallami fursunoni

Published

on

Babban jojin jihar nan mai shari’a Nura Umar ya sallami wasu Fursinoni 35, wadanda aka tsare su ba bisa Ƙa’ida ba, a gidan gyaran hali na Goron Dutse.

Baba Jibo Ibrahim wanda shi ne mai magana da yawun kotunan kano ne ya fitar da sanarwar hakan.

Mai shari’a Nura Sagir Umar ya saki fursinonin a wata ziyarar kwanaki biyu da yake gudanarwa,a gidan gyaran hali na Goron Dutse.

Mai shari’a Nura ya ce, Kundin tsarin mulkin Najeria ya bashi dama na ziyartar gidajen gyaran hali a karkashin sashe na 1 daya cikin baka.

Haka kuma yana da ikon sakin duk wani Fursina da aka tsare ba bisa Ƙa’ida ba.

Sakin fursunonin ya biyo bayan matakin rage Cinkoson da ake samu a gidajen gyaran hali na Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!