Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aikin Allah: Sarkin Kano Murabus ya fitar da ɗaurarru daga gidan yari

Published

on

Mai martaba sarkin Kano murabus, Muhammadu Sanusi na biyu ya biyawa ɗaurararu 38 bashin da ake bin su, da kuɗin ya kai sama da miliyan 22.

Ɗaurarrun da ke gidan gyaran hali na kurmawa 14 ne aka biya musu naira miliyan 14, sai waɗanda ke gwauran dutse 24 da aka biya musu tarar miliyan bakwai.

Da yake miƙa kuɗaɗen Mujittafah Abubakar Abba Falaki a madadin sarkin Kano murabus ya ce, an biya kuɗin ne fisabilillahi, kuma wani bangare ne na bikin cika shekaru 60 da Muhammadu Sanusin yayi.

Tuni dai aka fara tantance ɗaurarrun da suka rabauta, domin miƙa su ga iyalansu kamar yadda mai magana da yawun gidajen yari na Kano Musbahu Lawal Kofar Nasarawa ya tabbatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!