Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu a kan hanyar Oshodi-Apapa,jihar Lagos

Published

on

Mutane uku ne suka rasa rayukan su yayin da wasu shida suka samu raunuka yayin wani hadari da ya auku kusa da tashar motoci da ke Ilasamaja a kan hanyar Oshodi-Apapa a jihar Lagos.

Guda daga cikin ma’aikatan kamfanin Makasa Sun Limited da ke gudanar da aikin ginin wata Gadar sama da aka bayyana sunan sa da Odejayi Adebola da kuma wani dan kasuwa da ke gudanar da kasuwanci a yankin, na cikin wadanda suka rasa rayukan su.

Hadarin dai ya faru ne a lokacin da wata babbar motar diban kaya ta yi karo da gadar da ake ginawa a wannan wajen wanda kuma hakan ya sanya wata motar safa ta daki bayan motar wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Rahotanni sun bayyana cewa motar na gudun wuce sa’a ne lamarin da ya sanya motar ta kwace daga hannun direban ta da misalin karfe 8 na safiyar yau.

Sai dai kuma ganau sun bayyana cewa mutanen da suka rasa rayukan su yayin hadarin, wanda kuma suka ce a take suka kira jami’an kashe gobara amma basu iso gurin akan lokaci ba

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!