Connect with us

Labarai

AKTH ya musanta bada ayyukan kwangila

Published

on

Asibitin koyarwa na Aminu Kano ya musanta jita jitar da ake yadawa cewa Asibitin zai bada ayyuka masu yawa ga ‘yan kwangila daban-daban.

Wannan na cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta asibitin Hauwa Muhammad Abdullahi ta fitar ga manema labarai a Larabar nan.

Sanarwar ta ce a yanzu haka asibitin ba shi da wata kwangila da zai iya bayarwa.

“’Dukkanin ayyukan kwangilar da ake yi a cikin asibitin AKTH gwamnatin tarayya ce ta ke bayar da su”.

kazalika sanarwar ta gargadi al’umma da su guji jefa kan su cikin rigima tare da kaucewa fadawa hannun ’yan damfara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!