Connect with us

Kiwon Lafiya

Akwai bukakatar samar da tsarin bada lafiya mai nagarta ga marasa lafiya-hukumar asibitoci

Published

on

Hukumar gudanarwar Asibitocin jihar Kano ta bukaci Asibitocin gwamnatin jiha da su samar da tsarin bada lafiya mai nagarta ga marasa lafiyan fadin jihar Kano.

Shugaban hukumar Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi, yayin taron watannin ukun karshen shekara, domin tattaunawa kan batutuwan da suka faru a bangaren lafiya a baya.

Shugaban hukumar, wanda ya samu wakilcin daraktan sashen lura da aikin likitanci na hukumar Dakta Muhammad Dahiru Shehu, ya ce ya lura da cewa akwai bukatar inganta tsarin kula da marasa lafiya a Asibitocin jihar Kano baki daya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!