Labarai
Akwai bukatar ci gaba da fadakarwa kan cin zarafin mata da kananan Yara- AOWD
Kungiyar tallafa wa marayu da marasa karfi ta Alkhairi Orphanage And Human Development AOWD, ta jaddada kudurinta na magance cin zarafin ‘ya’ya Mata da Kananan Yara.
Shugabar kungiyar Ambasada Rukayya Abdurrahman, ce ta bayyana hakan yayin taron wayar da kan dalibai kan dakile Cin zarafi tsakanin mata da maza da kungiyar ta gudanar ga daliban makarantar Sakandaren GGSS Gwammaja 1 da ke jihar Kano.
Ambasada Rukayya Abdurrahman, ta ce, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su kara kaimi wajen dakile dabi’ar cin Zarafin Mata da kananan Yara domin kara samun ci gaba da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Haka kuma shugabar ta yaba da yadda dalibai da malaman Makarantar suka bai wa taron hadin kai, tare da yin fatan shawo kan wannan matsala.
A nasu bangaren, wani dalibi da kuma guda cikin malaman makarantar, sun bayyana farin cikinsu bisa shirya wannan taro, inda suka sha alwashin zama jakadun kungiyar wajen fadakar da al’umma don dakile wannan matsala.
A yayin taron dai, shugabar kungiyar ta Alkhairi Orphanage And Human Development, ta kuma ce, akwai bukatar ci gaba da wayar da kan al’umma kan dakile cin zarafin jinsi a ko da yaushe ba sai a iya makon da majalisar dinki duniya ta ware ba da ake gudanarwa a tsakanin ranakun 25 ga Nuwamba zuwa 10 watan Disamban kowacce shekara ba.
You must be logged in to post a comment Login