Connect with us

ilimi

Kano ta zama koma baya a fagen ilimin kimiyya da fasaha – ASUP

Published

on

Ƙungiyar malaman kwalejin kimiyya ta ASUP ta ce, jihar Kano ta zama koma baya a fagen ilimin kimiyya da fasaha.

Mai magana da yawun ƙungiyar Abdullahi Yalwa ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kano.

Ya ce, sun yi takaici matuƙa da yadda suka riski kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano a cikin mawuyacin hali.

Abdullahi Yalwa ya ƙara da cewa, gazawar Gwamnati ce ya janyo harkar ilimi ke ƙara taɓarɓarewa.

A ƙarshe ya bayyana cewar, matuƙar Gwamnatin ba za ta riƙa mutunta bukatunsu ba, to ya zama dole su riƙa tsunduma yajin aiki kamar sauran ƙungiyoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!