Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ni ne halastaccen shugaban jam’iyyar APC a Kano–Danzago

Published

on

Guda cikin Mambobin jami’iyyar APC a Kano tsagin G7 da Malam Ibrahim Shekara ke jagoranta Ahmad Haruna Zago ya ce har yanzu shi ne halastaccen shugaban APC a Kano.

Ahmadu Haruna Zago ya bayyana haka ne yayin taron ganawa da shugabannin jami’iyyar ta APC na Kano tsagin G7, wanda ya gudana a ranar Asabar 19 ga Fabrairun 2022 a nan Kano.

Dan Zago ya ce “hukuncin da Kuto ta ayyana a makon da muke shirin ban kwana da shi, bai nuna tsagin da muke adawa da su zasu jagoranci jami’iyyar ba, kuma bai nuna an ciremu daga shugabancin jami’iyyar ba,”

“Hukuncin ya nuna kawai a koma jami’iyya ta gudanar da nata aikin domin warware duka matsalolin da ke wakana ,” a cewar Dan Zago.

Haruna Zago ya karada cewa tuni suka gama tattara takardu domin daukaka kara zuwa kotun koli wanda suke sa ran samun adalci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!