Labarai
Akwai son zuciya wajen dakatar da shugaban hukumar Anti-kwarafshin – CISLAC
Ƙungiyar da ke bin diddigi kan ayyukan majalisu (CISLAC), ta ce, ta yi mamaki matuƙa kan yadda aka dakatar da shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimingado, wadda majalisar dokokin Kano ta yi, tare kuma da naɗa mai riƙon mukamin hukumar da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
Babban jami’in ƙungiyar anan Kano, kwamared Nura Iro Ma’aji shine ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar Freedom rediyo da safiyar yau litinin.
Ma’aji ya ce, ƙungiyar CISLAC ba ta goyon bayan ɗaukar wannan mataki saboda ba abi hanyoyin da suka dace kafin ɗaukar matakin.
‘‘Ina tabbatar da cewa idan har za a tsaurara bincike kan wannan al’amari, ina da yaƙinin za a gano cewa, tsakanin gwamnati da Muhuyi kowannensu yana da laifi’’.
“Idan aka nazarci yadda tun farko aka naɗa shi (Muhyi Magaji) kan wannan muƙami za a gano cewa ya saɓawa doka’’ a cewar Nura Iro Ma’aji.
Nura Iro Ma’aji ya kuma ce, yana kyautata zaton akwai wani abu da ake son ɓoyewa shi ya sanya aka yi gaggauwar ɗaukar wannan mataki Muhyi Magaji.
Sai dai ya ce duk da cewa, ba abi ka’ido ba tun da fari wajen naɗa Muhyi Magaji Rimingado kan muƙamin na shugabancin hukumar anti-kwarafshin ta jihar Kano, amma ba ko shakka ya taka rawar gani wajen daƙile ayyukan cin hanci da rashawa a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login