Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Akwai sauran rina-akaba wajen kakkabe cin hanci a Najeriya- CISLAC

Published

on

Kungiyar CISLAC tace har yanzu akwai sauran rina-akaba kan batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaban kasa  Muhammadu Buhari ke ikararin gwamnati ta himmatu akai domin dakile matsalar.

Kwamared Nura Iro ma’aji na KUNGIYAR CISLAC ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Duniyar mu a yau na gidan Radio Freedom daya mayar da hankali kan rahotan da Transparency International ta fitar na karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya a makon daya gabata.

Nura Iro Ma’aji ya kara da cewa kamata yayi idan aka fitar da rahoto na karuwar cin hanci da rashawa da kungiyoyi masu zaman kansu keyi ya rika tallafawa gwamnati wajen gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin bawai su rika musantawa ba.

Hukumomi kadai ba za su iya magance cin hanci da rashawa ba- EFCC

Sai da binciken kwakwaf za’a shawo kan matsalar cin hanci -Anas Aremauyaw

Ministan yada labarai yace gwamnatin Buhari zata yaki cin hanci da rashawa

A nasa bangaren Ambasada Aliyu Lawan Saulawa ta cikin shirin cewa yayi wadannan rahotanni da kungiyoyin ke fitarwa na karuwa cinhanci da rashawa a Najeriya ba komai bane face son zuciya irin tasu da kuma biyan bukatun iyayen gidansu.

 

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito dukkannin bakin a cikin shirin sunyi kira ga masu rike da madafin iko akan suji tsoron Allah su kuma daina kwashe dukiyar Al’ummar Najeriya domin bakomai hakan zai jawa kasar nan ba face koma baya ta kowacce fuska.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!