Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai yiwuwar ƙara sauke ministoci – Gwamnatin tarayya

Published

on

Fadar shugaban ƙasa ta ce, akwai yiwuwa sake sauke wasu ministoci nan ba da dadewa ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwa.

Adesina ya ce, akwai yiwuwar shugaban Buhari ya sake sallamar wasu daga cikin ministocin na sa.

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban Muhammadu Buhari ya jagoranci majalisar zartarwa ta kasa karo na farko tun bayan da ya sallami minisitocin sa biyu.

Buhari ya ce, gwamnatin sa za ta ci gaba da bibiyar ayyukan da hukumomi ke aiwatarwa don gano matsalolin da suke ciki da kuma ɗaukan matak, a wani yunƙuri na kawo ci gaba a ƙasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!