Connect with us

Jigawa

Yan sanda a Jigawa sun tabbatar da mutuwar wata mata da mijinta ya soka mata wuka

Published

on

Rundunar ‘yan sanda Jihar Jigawa ta cafke wani magidanci da ake zargi da sanadiyyar mutuwar matarsa.

Mai magana da yawun rundunar ASP Lawan Shisu ne ya bayyana hakan a daren jiya Laraba 08 ga Satumbar shekarar 2021 ga manema labarai.

Badaru ya biya ‘yan Fanshon Jigawa hakkin su

Lawan Shisu ya ce lamarin ya faru ne a Kauyen Makadi dake Karamar hukumar’Ba’bura a jihar ta Jigawa, inda mijin matar Abdulmumin ya sokawa matar ta sa mai suna Sahura wuka hakan kuma ya yi sanadiyyar mutuwar ta.

Jami’in hurda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Jigawa ASP Lawan Shisu na gargadin jama’a kan su guji daukar doka a hannun su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!