Connect with us

Labarai

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da Yobe- NIMET

Published

on

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da Yobe, kamar yadda Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar a wani hasashen yanayi da ta fitar a shafinta na X.

Hukumar ta ce tsawa da ruwan sama matsakaici na iya sauka a wasu sassan arewacin kasar nan wadda zai iya haddasa ambaliyar ruwan.
NiMet ta bayyana cewa da safiyar yau Talata, ana sa ran ruwan sama a jihohin Borno, Yobe, Jigawa, Gombe, Bauchi, Adamawa, Kaduna da Taraba.

Hakanan, da yamma zuwa dare, ana sa ran yawancin jihohin Arewa za su ci gaba da samun ruwan sama tare da iska da tsawa.

A tsakiyar Najeriya kuwa, hasashen ya nuna cewa za a samu yanayin giragizai da safe, sannan da yamma za a samu ruwan sama matsakaici a wasu sassan Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara, Neja, Filato da kuma babban birnin tarayya Abuja.

NiMet ta kuma bayyana cewa a Kudancin Najeriya, da safe ana sa ran yanayi mai giragizai tare da yiwuwar ruwan sama a wurare kaɗan, yayin da a Yammaci ake hasashen ruwan sama a lokuta daban-daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!