Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a samu mamakon ruwan sama a Kano tsawon kwanaki 3 da ma wasu jihohi – NiMET

Published

on

Hukumar Kula da yanayi ta ƙasa NiMET ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske a Kano na tsawon kwanaki 3.

NiMET ta ce, za a samu mamakon ruwan har a wasu sassan ƙasar nan da dama kamar yadda ta fitar cikin wata sanarwa.

A cewar NiMET a waɗannan kwanakin jihohin Kano, Bauchi, Jigawa, Katsina, Zamfara, Kaduna, Kebbi, Sokoto da Neja za su fuskanci mamakon ruwan saman.

Sai dai ta ce, za a samu matsakaici ruwan saman a jihohin Yobe, Kwara, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Taraba, Adamawa, Ekiti, Filato, Nasarawa da Benue, Enugu, Ebonyi, Anambra, Abia, Imo, Cross River da Akwa Ibom.

NiMet ta yi gargaɗin cewa, akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa musamman a jihohin da ake sa ran samun mamakon ruwan saman, da zai iya haifar da karyewar gadoji, rushewar gidaje da kuma hana tashin jirage.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!