Labarai
Akwai yiwar sake kai hari a Sakandiren ‘yan mata na Dapchi
Kungiyar ‘iyaye da malamai kuma kumgiyar da aka sacewa ‘ya’ya ta Dapchi ta rufe sun rufe makarantar sakandiren kimiyya da fasaha ta Dapchi dake jihar Yobe kan fargabar akwai yuwar sake kai hari da kungiyar Boko Haram ke shirin yi.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan sa ta ce kungiyar ta rufe makarantar ne biyoi bayan umarnin da hukumomin tsaro suka bayar na kwashe daliban mata har sau uku bayan da suka sami rahoton akwai yuwar a sake kai hari tare da sace daliban na Dapchi.
Da yake tabbatar da rufe makarantar shugaban kujngiyar Iyaye da daliban makarantar, Alhaji Bashir Manzo ya ce kwamadan rudunar JTF a yankin, ya kira kungiyar har sau uku yana umartar da su kwashe ‘ya’yan su a makarantar zuwa gidan sarkin yankin ko wasu masu rike da masarautun gargajiya, amma kuma daga bisani suke ganin cewar kamata yayi a rufe makarantar baki daya.