Connect with us

Labarai

Akwai yiwar sake kai hari a Sakandiren ‘yan mata na Dapchi

Published

on

Kungiyar ‘iyaye da malamai kuma kumgiyar da aka sacewa ‘ya’ya ta Dapchi ta rufe sun  rufe makarantar sakandiren kimiyya da fasaha ta Dapchi dake jihar Yobe kan fargabar akwai yuwar sake kai hari da kungiyar Boko Haram ke shirin yi.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan sa ta ce kungiyar ta rufe makarantar ne biyoi bayan umarnin da hukumomin tsaro suka bayar na kwashe daliban mata har sau uku bayan da suka sami rahoton akwai yuwar a sake kai hari tare da sace daliban na Dapchi.

Da yake tabbatar da rufe makarantar shugaban kujngiyar Iyaye da daliban makarantar, Alhaji Bashir Manzo ya ce kwamadan rudunar JTF a yankin, ya kira kungiyar har sau uku yana umartar da su kwashe ‘ya’yan su a makarantar zuwa gidan sarkin  yankin ko wasu masu rike da masarautun gargajiya, amma kuma daga bisani suke ganin cewar kamata yayi a rufe makarantar baki daya.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,987 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!