Labarai
Al’amura sun tsaya cak a ma’aikatar ruwa ta Kano
Al’amuran mulki sun tsaya cak a ma’aikatar samar da ruwansha ta jihar Kano, sakamakon rashin biyan ma’aikatan hukumar mafi karashin albashi da hukumar ta gaza biya tsahon watanni.
Da tsakar ranar yau juma’a ne dai fusatattun ma’aikatan hukumar suka garkame kofar shiga hukumar, babu shiga ba fita sakamakon rashin biyan su sabon mafi karancin albashi da suke ta faman jira a biya su.
Alhaji Shehu Lawan shine shugaban hadaddiyar kungiyar ma’aikatan ruwa reshen jihar Kano, a yayin zantawarsa da Freedom Radio ya bayyana cewa sun tara sama da naira miliyan Hamsin da Tara a amma biyansu albashi ya faskara sai dai ayi tayi musu alkawari.
“baki daya kudin da ake biyan ma’aikatan bai wuce naira miliyan sittin da daya ba amma biyan su ya faskara har izuwa yanzu” a cewar sa.
Alhaji Shehu Lawan ya kara da cewa abinda ya tunzura ma’aikatan daukar wannan mataki shine yadda aka biya su da tsohon albashin su na baya wanda yasa ma’aikatan na su suka tayar masa da hankali akan hakkin su.
Karanta karin labarai:
Mace ta zubawa dan kishiyarta ruwan zafi a Kano
Ma’aikatar ruwa sha ta kasa ta musanta zargin sayar da madatsan kasar
Freedom Radio tayi kokarin jin tabakin mahukuntan ma’aikatar ruwan ta jihar Kano amma abin yaci tura.
You must be logged in to post a comment Login