Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Alhaji Tanimu Turaki:Na fi kowa cancanta shugabanci kasar nan

Published

on

Tsohon Ministan ayyuka na musamman Alhaji Tanimu Turaki ya shaida cewa shi ne mafi cancanta da shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa, la’akari da cewa ya taka matakin Ilimin da shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kai ba.

Tanimu Turaki wanda Lauya ne mai lambar kwarewa ta SAN ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya kai ziyara Shelkwatar Jam’iyyarsa ta PDP, da yake muradin ta tsayar da shi takara a zaben badi.

Ya kuma shaidawa Kwamitin gudanarwar Jam’iyyar na kasa cewa yana da nagarta da tsoron All.. irin na shugaban kasa Buhari, da ake ta karadi a kai, hasali ma yana da wasu abubuwan da Buharin ya gaza a kansu.

Har ila yau ya bayyana cewa ‘yanNajeriya suna cikin halin damuwa da kaka-naka-yi, a don haka akwai bukata PDP ta jajirce wajen ganin ta tsayar da ingantaccen dantaka da zai fafata da Jam’iyya mai mulki ta APC.

Tanimu Turaki ya ce tun bayan kayin da PDP ta sha a hannun APC a zaben shekarar 2015, suka yi karatun ta nutsu inda suke fatan sake darewa kan karagar mulkin Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!