Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Filato:Akalla mutum 10 ne suka mutu yayin wasu hare-hare biyu

Published

on

Akalla mutum 10 ne su ka mutu yayin wasu hare-hare biyu da aka kai kananan hukumomin Mangu da Barkin Ladi a Jihar Filato a karshen makon da ya gabata.

Hare-haren sun tilasta jami’an tsaron Operation Safe Haven mayar da Shelkwatarsu Barkin Ladi don kawo karshen matsalar.

Mutum 6 ne dai suka mutu a harin da aka kai Mangu a daren Asabar yayin da 4 suka mutu a makamancin harin a Barkin Ladi a jiya Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar ta Operation Safe Heaven Manjo Adam Umar ya tabbatar da faruwar al’amarin, duk kuwa da matakan tsaron da aka tsaurara, ciki kuwa har da dokar hana zirga-zirga da aka sanya.

Ya kara da cewa dakarunsu da ke yankin Dorowa ne suka sanar da su cewa mutane daga Mararrabar Kantoma a karamar hukumar Barkin Ladi sun kirasu suna shaida musu cewa wasu ‘yan-bindiga sun far mu su.

Manjo Adam Umar ya bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya da juna, kuma su a matsayin jami’an tsaro za su ci gaba da aikinsu yadda ya dace don kyautata tsaro a garin da ma sauran wuraren da ke fuskantar matsala.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!