Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Wasu mata hudu sun mutu sanadiyar kifewar kwale-kwale

Published

on

Wani Kwale-kwale da ya kife a cikin ruwa a karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ‘yan-mata hudu.

‘Yan-matan da hatsarin ya ritsa da su su ne Yasira Sulaiman mai 16 da Safara’u Sa’idu mai shekaru 16, sai Nana Firdausi Ibrahim ‘yar shekaru 16 da kuma Zakiyya Isiya mai shekaru 17.

Lamarin dai ya faru ne a Dam din Mashiga lokacin da ‘yan-matan su ka hau Kwale-Kwalen domin wani Kauye da ke Makwabtaka da su domin sayen Zogale.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan-sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa ‘yan-matan sun fito ne daga kauyen Dan Zango.

Ya kuma kara da cewa wasu mutane ne suka kaiwa ‘yan-matan agaji har suka ceto guda daga cikinsu mai suna Maryam Zubairu mai shekaru 13, tare da direban Kwal-kwalen.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!