Labarai
Ali Ndume ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ya ke son nadawa

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin Shekarar 1999 ya tanada.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar dattawa ta karɓi jerin sunayen waɗanda shugaba Tinubu ke neman ya naɗa, waɗanda aka miƙa wa kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje domin tantance wa
Sai dai Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce jerin sunayen ya ci karo da sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin ƙasar nan wanda ya buƙaci a yi daidaito tsakanin ɓangarorin Najeriya wurin bayar da muƙaimai.
You must be logged in to post a comment Login