Labarai
Tinubu ya cire sunan Maryam Shattima daga jerin sunayen Ministocinsa
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/08/Screenshot_20230804-190520.png)
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan Dr. Mairiga Mahmud domin maye gurbin Maryam Shetty daga Kano wadda aka tura sunanta a ranar Larabar data gabata.
Tinubu ya aike da sunayen ne ta cikin wata wasika da ya aikewa majalisar dattawa kuma Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya Karanta a zaman majalisar na yau juma’a
Haka zalika Bola Ahmad Tinubun ya aikewa majalisar dattawa sunan tsohon Ministan ƙwadago na kasa Festus Keyamo domin amincewa da shi don nada shi a matsayin minista.
You must be logged in to post a comment Login