Labarai
Alkhairi Orphanage ta gudanar da bikin ranar ilimin ƴaƴa mata

Ƙungiyar tallafa wa marayu da Mata ta Alkhairi Orphanage and Women Development, tare da abokan haɗin gwiwarta, sun gudanar da bikin Ranar ilimin ƴaƴa mata na Duniya na bana a yau Laraba, inda aka raba kyautar audugar mata ga mahalarta taron don kula da kansu.
Taron wanda aka gudanar a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta yan mata ta Danbare a nan Kano mai taken Muhimmancin Ilimi ga ‘Yaya Mata, ya samu halartar kungiyoyi da dama da suka haɗa da Network for Youth Enlightenment and Development da K-SAFE da CSACEFA da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta ƙasa NHRC.
Da ta ke jawabi kan maƙasudin taron, Babbar Daraktar ƙungiyar ta Alkhairi Orphanage Kwamared Rukayya Abdulrahman, ta jaddada cewa ilimi shi ne makamin da zai sauya rayuwar ‘yaya mata.
Haka kuma, ta bayyana cewa ƙarfafa wa ‘yaya mata gwiwar neman ilimi shi ne tushen ci gaban al’umma, yana mai kiran kungiyoyi da gwamnati da su ci gaba da haɗa kai wajen samar da dama da daidaiton jinsi a tsakanin matasa.
A nasu ɓangaren, wasu daga cikin ɗaliban da suka halarci taron, sun bayyana farin cikinsu bisa shirya taron, tare da yaba wa ƙungiyoyin.
A nasa ɓangaren, Babban Daraktan Network for Youth Enlightenment and Development, Abdulsalaam Haruna, ƴa buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta ƙara ƙoƙari wajen ganin ta rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Haka kuma ya bayyana cewa, shirya irin wannan taro, zai taimaka sosai wajen faɗakar da ƴaƴa mata irin muhimmancin da yin karatunsu ke da shi musamman ma wajen kula da kansu tare da yi musu jagora a rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login