Kiwon Lafiya
Alkhairi Orphanage ta shirya Bikin makon abinci na Duniya

Yayin da aka fara gudanar da bikin makon abinci na duniya a yau Alhamis, Kungiyar Alkhairi Orphanage and Women Development AOWD da ke da ofishi a Kano, ta gudanar da taron wayar da kai da horaswa ga mata masu juna biyu da masu shayarwa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta a matakin farko na unguwar Dan-Tsinke da ke yanking Karamar Hukumar Tarauni.
A jawabinta, yayin taron, babbar Daraktar gudanarwar kungiyar Kwamared Rukayya Abdulrahman, ta bayyana cewa,Jaririn da aka shayar da nonon uwa kawai har tsawon watanni shida yakan fi ƙarfi da lafiya da kuma hazaka fiye da wanda ba a shayar da shi ba zallar Nono ba.
Haka kuma ta kara da cewa, manufar shiri ita ce ƙara wayar da kan mata irin muhimmancin shayar da jarirai nonon zalla na tsawon watanni shidan farko da koyar da ingantattun hanyoyin shayarwa da kuma faɗakarwa kan irin abincin da ya kamata a fara bai wa jarirai bayan watanni shida domin ƙara lafiyar uwa da jariri.
Kwamared Rukayya ta jaddada cewa yawaita shayar da nonon uwa kawai zai taimaka wajen gina jikin jarirai da kara musu lafiya tare da kare su daga kamuwa da cututtuka tare da rage yawan mutuwar mata da kuma kananan yara.
Wakilinmu Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, yayin taron, an koyar da mahalarta yadda ake dafa Tom Brown watau abinci mai gina jiki ga jarirai, sannan mata sama da 50 sun amfana da kunshin Tom Brown domin amfani da shi a gida.
Bugu da ƙari, AOWD ta gudanar da gwajin abinci mai gina jiki ga jarirai ‘yan watanni shida da suka haura, tare da tallafin kwararru daga Highland quality Education Consultancy Services.
You must be logged in to post a comment Login