Labarai
Allah ya yi wa fitacciyar jarumar masana’antar Kannywood Daso Rasuwa
Allah ya yiwa shahararriyar Jaruma a masana’antar shirya Fina-Finai ta Kennywood Hajiya Saratu Gidado da akafi Sani da suna Daso rasuwa.
Ta rasu a yau Talata 9 ga watan Afrilun shekarar 2024 da ya yi daidai da 30 ga watan Ramadana Hijra ta 1445.
Dan uwa ga marigayiyar Alhaji Mustafa Ibrahim Ci gari mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin tafiye tafiye da shakatawa ya tabbatarwa da Freedom Radiyo rasuwar ta ta.
Inda ya ce ” Anyi hira da yta da daddare inda ta shaidawa iyalinta cewa kowa yaje ya kwanta da Asubahin wannan ranama da Ita aka yi sahur dan daukar Azumi, sai da safe da akaji shiru bata fitoba aka bude dakin nata a nan ne akaga gawarta”.
Rahotanni dai sun yi nuni da cewa Daso bata taba haihuwaba, Kuma ta rasu ta na da shekaru 56.
Da fatan Allah ya ji kanta da Rahama Ameen Summa Ameen.
You must be logged in to post a comment Login