Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai tsaye: Ana gudanar da jana’izar Marigayiya Saratu Daso

Published

on

Yanzu haka ana gudanar da jana’izar Marigayiya fitacciyar ƴar masana’antar Kannywood Saratu Gidado, da aka fi sani smda Daso, wadda rasuwa wayewar garin yau Talata.

Yanzu haka dai an kammala yi wa marigayiyar Sallah a harabar gidan Sarkin Kano inda aka wuce maƙabarta domin binne ta.

Rahotonni sun bayyana cewa marigayiyar ta rasu ne tana da shekaru 56 a duniya.

A zantawar Freedom Radio da ƙanin ga marigayiyar Mustapha Ibrahim Ci Gari, ya tabbatar da rasuwar tata ya na mai cewa za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin yau Talata.

An haifi marigayi Saratu Gidado ne a ranar 17 ga watan Janairun shekarar 1968, inda ta shafe fiye da shekaru 20 tana taka rawa a masana’antar Kannywood.

Da fatan Allah ya jiƙanta da gafara ya kuma bai wa al’ummar Musulmi jure rashinta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!