Kaduna
Al’ummar da ke amfani da babbar hanyar da ke a Nnamdi Azikiwe Bypass a garin Kaduna na ci gaba da kokawa kan jinkirin kammala aikin titin

Alummar da ke amfani da babbar hanyar da ke a Nnamdi Azikiwe Bypass a nan tsakiyar garin Kaduna, na ci gaba da kokawa, kan jinkirin da ake ci gaba da samu, na kammala aikin.
Al’ummar da Freedom Radio Kaduna ta zanta dasu sun nuna damuwarsu na wahalhalun da haddurra da suke fuskanta da yake sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyin al’umma a kullum a wannan titi, kamar yadda wakiliyarmu Radiya Salis, ta ruwaito.
You must be logged in to post a comment Login