Connect with us

Labarai

Al’ummar unguwar Shekar Mai daki sun yi tayin gidajen su ga Dagaci

Published

on

Mazauna unguwar Shekar Mai daki dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano, sun yi tayin gidajen su ga dagacin yankin Malam Badamasi Muhammad.

Tayin ya biyo bayan kin jinin sababbin zuwa unguwar da suke zargin dagacin na yi.

Wasu mazauna unguwar sun shaidawa Freedom Radio cewa dagacin yana nuna musu kyama da wariya a matsayin su na baki, wadanda suka mallaki gidaje a wurin ba ‘yan asalin yankin ba.

Har ila yau, sun ce dagacin na taka rawa wajen dakile musu damarmaki da suke samu.

Wakilin mu Yusuf Ali Abdallah ya garzaya har gidan dagacin domin jin ta bakin sa amma ya ce a bashi lokaci, zuwa karfe biyar na yamma.

Kuma wakilin na mu yayi kokarin jin ta bakin dagacin a lokacin da ya bayar amma abin ya gagara.

Karin labarai:

Dagaci ya gano maboyar batagari a Kano

‘Yan garkuwa sun sace dagaci a Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,289 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!