Labarai
Ambaliyar Ruwa: A bana ba ma fargabar samun ambaliyar ruwa a Kano – Dakta Getso.
Gwamnatin jihar Kano ta ce, a bana bata da fargabar samun ambaliyar ruwa a sassan jihar.
A cewar gwamnatin, nan ba da dadewa ba jihar za ta fita daga cikin matsalar zubar da shara barkatai wanda hakan ne ke haifar da matsalar.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan, lokacin da yake zagayen duban yadda gangamin yashe magudanan ruwa ke gudana a sassan jihar Kano.
“ina tabbatarwa da al’ummar jihar Kano, cewa a bana bama fargabar samun ambaliyar ruwa, domin kuwa gangamin yashe magudanar ruwa da muke yi yayi tasiri musamman yadda mutane ke ta yin aikin gayya, wanda hakan ne ya sa cikin mako hudu da aka fara gangamin mun samu nasarar kwashe shara tifa dubu daya” a cewar Getso.
Dakta Getso ya ce, an samu nasarar ne ta hanyar karbar kiraye-kirayen da gwamnati ke yiwa al’umma na su rika ayyukan gayya a unguwannin su don kiyaye ambaliyar ruwa.
“babban kalubalen dai shi ne yadda mutane basa sanar da hukumomi cewar za su yi aikin gayya, don a basu gudunmawar kayan aiki, da sanin cewa da zarar sun fito da sharar aje a kwashe” inji kkwamishinan muhalli.
You must be logged in to post a comment Login