Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ambaliyar ruwa tayi awan gaba da gawarwaki a wata makabarta a jihar Yobe

Published

on

Ambaliyar ruwan sama da aka shafe kwanaki a na yi, ta yi sanadiyyar ruftawar kaburbura da dama a karamar hukumar Gashua dake jihar Yobe.

Alhaji Kabiru Bulama-Bukar, Jami’in cigaban Al’umar karamar hukumar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Talata 13 ga watan Yulin 2021.

Ya kuma ce, an fara ruwan saman ne tun daga ranar 9 ga watan na Yuli har zuwa ranar 12 ga watan, lamarin da yayi sanadiyyar bayyana wasu gawarwaki a makabartar.

Bulama-Bukar ya ce, “Mun samu ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin garin Gashua, yanzu haka gine-gine da dama sun lalace kuma makabartarmu ta rufta.”

“Da zaran mun kammala tantance barnar da mutanen da abin ya shafa, za mu gabatar da rahotonmu ga Hukumar ba da Agajin Gaggawa da majalisar jihar don daukar mataki,” in ji shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!