Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ambaliyar ruwa: An kaddamar da gangamin yashe magudanan ruwa a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin gangamin yashe magudanan ruwa karkashin kamfanin sarrafa shara mai zaman kansa anan Kano.

Aikin wanda kwamishinan muhalli na jihar Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya jagoranta, wanda aka fara yashe magudanar ruwan da ke shatale-talen gidan Baban Gwari.

Dakta Getso ya ce, ma’aikatar muhalli za ta tabbatar da an yashe dukkanin magudanan ruwan da ke fadin jihar nan domin kiyaye abkuwar ambaliyar ruwa da kuma tseratar da rayukan al’umma da dukiyoyin su.

“Tun bayan da muka samu rahoton hukumar hasashen masana yanayi da ta bayyana jihar Kano cikin jerin jihohin da za su fuskanci ambaliyar ruwa muka fara shirin dakile matsalar tun da wuri, don gujewa shiga yanayin da muka fuskanta a bara” a cewar Getso.

Getso ya kuma ce, an fara gangamin ne gaba in zuwan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da zai zo ya kaddamar da shirin yin aiki da kamfanin sarrafa shara mai zaman kan sa da aka kulla yarjejeniya da shi.

Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano REMASAB Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo ya tabbatar da cewa hukumarsu za ta bai wa kamfanin dukkanin hadin kai domin ganin jihar Kano ta fita daga matsalar ambaliyar ruwa.

“Mun ga yadda jihar Kano ta kasance a shekarar bara sakamakon ambaliyar ruwa, wannan ne ya sa muka zabi shatale-talen gidan baban gwari don dada aiwatar da aikin, kasancewar wajen yafi ko’ina matsala a lokacin damuna” inji Gwarzo.

Shugaban kamfanin sarrafa sharar da aka kulla yarjejeniya da shi Alhaji Bashir Namadina ya ce kamfanin na su zai bi dukkanin manya manyan magudanan ruwan jihar tare da yashe su kafin faduwar damunar bana.

“Wannan aiki da za mu yi na yashe magudanan ruwa so-min-tabi- ne kuma kyauta za mu yi don gwamnati da al’umma su fara ganin kamun ludayin mu” a cewar Namadina.

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano na gargadin al’umma da su guji zubar da shara barkatai domin kuwa doka zata fara aiki nan take ga masu wannan dabi’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!