Labarai
Ambaliyar ruwa ta shafi jihohin Najeriya 12- hukumar NEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ayyana jihohin kasar nan goma 12 da ke rayuwa a gabar kogin Niger da Benue a matsayin wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa fiye da sauran jihohin kasar nan.
Shugaban hukumar ta NEMA Alhaji Mustapha Maihaja ne ya bayyana hakan yayin taron hukumar na wata-wata da zauren masu lura da al’amuran tsaro da jami’in yada labaran hukumar ke gudanarwa.
Ya ce tuni aka kididdige irin asarar da aka yi a mafi yawa daga cikni jihohin kasar nan da suka samu mamakon ruwan sama a bana, da ya yi sanadiyyar kogunanan Niger da Benue suka yi ambaliya.
Ya kuma ayyana sunayen jihohin Benue da Kogi da Niger da kuma Kwara sai jihar Anambra da Benue da Delta da Bayelsa da Rivers sai kuma Adamawa da Kebbi da Taraba a matsayin wadanda suka fi sauran jihohin kasar kamuwa da wannan iftila’i.
A cewar Mustapha mai Haja matakin da aka dauka tun da fari kafin aukuwar al’amarin shi ne ya taimaka wajen dakile yawaitar matsalar kamar yadda ya faru a shekarar 2012.