Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rahoto kan wasu al’amuran da suka shafi muhalli a bara

Published

on

  • A shekarar ne majalisar dokokin Kano ta sahale dokar kare gurbatar yanayi.

 

  • A 2022 jihohin Kano, Kwara, Ribas, Cross Riba, Bayelsa, Delta, Kogi, Yobe, Kebbi, Nassarawa, Adamawa, Neja, Bauchi, Zamfara, Sakkwato da kuma Jigawa.

 

A shekarar da muka yi ban kwana da ita ta 2022, al’amura da dama sun faru a fannin harkokin muhalli musamman ta fannin dumamar yanayi, ambaliyar ruwa, tsawa, zaizayar kasa, fari da dai saurarnsu.

Kasashen duniya da dama sun sha fama da matsalar ambaliyar ruwa a 2022 sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi ta tafkawa, abin da ya haifar da shafewar yankuna a kasashen duniya daban-daban.

Kasashe da dama a nahiyar Turai irin su Ingila, Faransa, da Jamus, sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa tare da lalacewar gidaje da gonaki.

Idan muka dubi yankin Arewacin Amurka kuwa, kasashe irin su Canada da Maxico sun fuskanci ambaliyar ruwa da tsawa a yankuna daban-daban, baya ga lalacewar gonaki.

Haka abin yake a kudancin Amurka, domin kuwa ambaliyar ruwan ta shafi kasashe irin su Brazil da Argentina, inda sama da mutane 50 suka rasa rayukansu a cikin wata guda sakamakon mamakon ruwan sama, a Uruguay kuma wani mamakon ruwan sama da aka tafka na tsawon sa’a guda ya haifar da katsewar lantarki a yankuna da dama na kasar, da kuma cunkoson ababen hawa, wanda ya janyo aka kwashe mutane sama da 164 daga muhallansu zuwa wasu wuraren, baya ga karyewar bishiyoyi da turakun wutar lantarki.

A karshen watan Disamba ne kuma Amurka ta yi fama da wata dokar kankara da ta rinka daskarar da halittu.

A yankin Asia kuwa, mummunar ambaliyar ruwan da aka samu da ba a taba ganin irinta ba a shekarun baya-bayan nan, ita ce ta kasar Pakistan, domin kuwa a kididdigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar tare da hadin gwiwar hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, sun nuna cewa daga ranar 8 ga watan Nuwamban da ya gabata, sama da mutane miliyan 33 ne ambaliyar ruwan ta shafa a Pakisatan kuma suke bukatar agaji, yayin da mutane sama da dubu 1,739 suka rasa rayukansu, sai kuma mutane miliyan takwas da suka rasa muhallansu sanadiyyar ambaliyar ruwan.

Yadda al’ummar kasar Pakistan ke neman agaji kenan a yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye gidajen su.

A jawabin Firaministan kasar Shehbaz Sharif, ya bayyana ambaliyar ruwan a matsayin tashin hankali mafi muni da suka taba gani, wanda yar manuniya ce ga yadda ake fuskantar dumamar yanayi a fadin duniya, haka shi ma sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres ya ce ba a taba ganin ambaliyar ruwa mafi muni irin ta ba.

Haka kuma ambaliyar ta janyo karuwar talauci a kasar da kaso biyar da digo tara cikin 100, kuma ana fargabar sama da magidanta miliyan 1 da dubu dari 9 ne za su fada kangin talauci.

A kasar Afghanistan kuwa, ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 130 musamman a yankunan gabashin kasar, a inda ya haifar da barkewar cututtuka irin su kwalara, zazzabin cizon sauro, amai da gudawa, yunwa da dai sauransu.

A kasar India ma ambliyar ruwan ta mamaye yankuna da dama, musamman ma a arewa maso gabashin kasar, inda ambaliyar ruwan ta shafi sama da mutane miliyan 9, haka kuma sama da mutane dari uku ne suka rasa rayukansu.

Idan muka dawo nahiyar Afirka kuwa, kasashen Zimbabwe da Gini da Dimokradiyyar Congo sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, domin kuwa ko a watan Janairu kadai, rahoto ya nuna yadda mutane goma suka rasa rayukansu a Zimbabwe, yayin da gidaje sama dari 812 suka lalace, haka kuma makarantu 51 suka rushe, tituna da gadoji sama 15 suka lalace.

Yayin da a kasar Gini ambaliyar ta shafi mutane sama da 2,576, ciki kuwa har da kananan yara sama da 137.

A nan gida Najeriya kuwa, rahoton asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da kuma gwamnatin tarayya ya nuna cewa kimanin mutane dari 6 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a 2022, yayin da mutane sama da miliyan daya da dubu dari uku suka rasa muhallansu a jihohi 34 cikin 36 na kasar nan har da birnin tarayya Abuja, har ma ma’aikatar jin kai ta ce ba a taba ganin ambaliya mafi muni ba cikin shekaru 10 da suka gabata irin wannan.

Daga cikin jihohin da ambaliyar ta shafa sun hada da Kwara, Ribas, Cross Riba, Bayelsa, Delta, Kogi, Yobe, Kebbi, Nassarawa, Adamawa, Neja, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Jigawa da nan Kano.

Sauran sune: Edo, Lagos, Benue, Akwa Ibom, Anambra.

Kuma kimanin mutane miliyan 1 ambaliyar ta tilastawa barin muhallansu yayin da gidaje sama da dubu 82 suka lalace, sai gonaki da fadinsu ya kai kadada dubu 272 da suka shafe.

Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin da suka fuskanci mummunar ambaliyar ruwa, domin kuwa wani mamakon ruwan sama da aka yi ya yi sanadiyyar tashin garin Karnaya, tare da yin sanadiyyar rasa rayuka sama da 134 da kuma lalata dukiya da kimarta ta kai kimanin naira tiriliyan daya da biliyan 5, da kuma shafe gidaje da dama, kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar.

A wata kididdiga da UNICEF ta fitar, ta nuna cewa sama da mutane 257 ne suka rasu dalilin ambaliyar ruwa a jihar Jigawa, sai kuma sama da mutane 231 da suka rasa muhallansu baya ga shafewar gonaki.

Yadda al’ummar wadannan yankuna suka rinka neman taimako a wancan lokaci da ambaliyar ruwan ta raba su da muhallansu kenan.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/FILET.mp3?_=1

A nan Kano ma an samu ambaliya ruwa da ta shafi dukkan kananan hukumomin jihar 44, sai dai ta fi tasiri a kananan hukumomin Warawa, Wudil, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu da sauran su.

Yayin da a kwaryar Birnin Kano ambaliyar ruwan ta yi sanadiyyar asarar miliyoyin kudaden ‘yan kasuwar Kantin Kwari, da ta tafi da shaguna, sakamakon gine-ginen da aka yi a kan magudanar ruwa.

Haka kuma ambaliyar ruwan ta lalata gonaki sama da 14,496, sai kuma mutane 23 da suka rasa rayukansu a kananan hukumomi 25 na Kano.

To ko menene ke haifar da ambaliyar ruwan da ake samu a kowace shekara? Tambayar kenan da Freedom Radio ta yi wa masanin muhallin a Kwalejin koyar da harkokin tsafta da lafiya ta jihar Kano Dakta Bashir Bala Getso, ga kuma karin bayanin da ya yi.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/CEWA.mp3?_=2

Game da halin da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa suke ciki kuwa, mun tuntubi hukumar ba da agajin gaggawa ta Kano SEMA, inda shugabanta Kwamared Sale Aliyu Jili, ya ce.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/JILI.mp3?_=3

To ko wane mataki hukumomin da abin ya shafa za su dauka don kare afkuwar ambaliyar ruwan a nan gaba? Dakta Kabiru Ibrahim Getso shi ne kwamishinan muhalli na jihar Kano ga abinda ya ce.

https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2023/01/GETSO.mp3?_=4

A shekarar da muka yi bankwana da ita ta 2022 ne majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kare gurbatar yanayi, wadda kuma ba a jima ba gwamna Dr Abdullah Umar Ganduje ya sanya mata hannu domin fara amfani da ita.

Ana dai sa ran dokar za ta rika duba harkokin zaizayar kasa da ambaliyar ruwa da sauyin yanayi.

 

Rahoton: Madina Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!